1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Turai da Afurka

June 2, 2004

Kasashen Turai kan mayar da hankali ga al'amuran Afurka ne a daidai lokacin da nahiyar ke fama da kaka-nika-yi

https://p.dw.com/p/BvjC
Dangantakar Kasashen Turai da Afurka
Dangantakar Kasashen Turai da AfurkaHoto: AP

Ko da yake mutane kan mayar da hankalinsu sosai da sosai ga ire-iren hutunan da ake nunarwa ta gidajen telebijin ko mujallu da sauran kafofin yada labarai, amma a hakikatal-amari ire-iren abubuwan da ake nunarwa wani dan gutsure ne daga ainifin abin dake faruwa. Sai dai kuma muhimmin abu a game da wadannan hotuna Ya-Allah ta’asar dake wanzuwa ne a Darfur ko azabtar da fursinoni a kasar Iraki, muhimmin abu shi ne tasirin da wadannan hutuna ke yi a ra’ayin jama’a da kuma manufofi na siyasa. Wadannan hotuna ba kome ba ne illa kira a game da daukar matakai na gaggawa, amma abin takaici sai a rika lalube a cikin dufu ba tare da sanin ainifin bakin zaren warware rikicin dake akwai ba. Ana iya lura da wannan matsalar a dangantakar kasashe masu tasowa da kasashen yammaci dake da ci gaban masana’antu ko kuma dangantakar kasashen Turai, musamman ma Jamus da kasashen Afurka, inda zakarar babu wani takamaiman shirin da aka tanadar bisa manufa. Babban misali a nan shi ne rikicin kasar Kongo ko tabarbarewar al’amura a kasar Zimbabwe da kuma mawuyacin halin da ake ciki yanzu haka a yammacin kasar Sudan. Dukkan wadannan abubuwa suna masu yin nuni ne da irin naka-nika-yin da Jamus ta samu kanta a ciki a cikin tarihinta na bayan yakin duniya na biyu. Amma fa tuni wannan zamani ya shude, kuma wajibi ne Jamus da sauran kawayenta na Turai su fito fili su tantance ainifin alkiblar da suka fuskanta a dangantakarsu da kasashen Afurka. Duk cika bakin da aka saba yi na ba da fifiko ga matakan yaki da talauci ko nuna kazar-kazar wajen gabatar da taimakon gaggawa, kamar yadda lamarin yake a yanzun dangane da yammacin Sudan, ba su da ma’ana. Nahiyar Afurka tana da girman gaske kuma matsalolinta na da yawa ta yadda ya zama wajibi a tantance abubuwan da suka zama a’ala, wadanda za a ba su fifiko a fafutukar raya makomar wannan nahiya. Daga baya-bayan nan dai gaggan masana al’amuran Afurka sun shiga batu a game da manufofin tsaro da hadin kan kasa. Domin kuwa ita ma Afurka, daidai da sauran nahiyoyi na duniya, tana bukatar tsaro domin raya makomar kasashenta. Amma muddin kasashen Turai suka kuskura suka yi sako-sako da al’amuran nahiyar, kamar yadda Amurka ke sako-sako da al’amuran Yakin Gabas ta Tsakiya to kuwa ko ba dade ko ba jima za a gwammace kidi da karatu dangane da irin matsalolin da nahiyar Turai zata samu kanta a ciki. A halin yanzu haka zazzafan ra’ayi na akida Ya-Allah ta addini ce ko ta siyasa sai dada yaduwa yake a nahiyar Afurka kuma angizonsa ya fara kaiwa nahiyar Turai da ita kanta kasar Amurka. Ta la’akari da haka ya zama wajibi kasashen Turai abin da ya hada har da Jamus su natsu su gabatar da wani takamaiman shirin da zai taimaka wajen sassauta radadin matsalolin dake addabar kasashen Afurka, a maimakon ci gaba da rufa wa ‚yan cin hanci dake rike da madafun mulki a wadannan kasashe. Muddin an ci gaba akan haka to kuwa ba shakka za a wayi gari murna ta koma ciki, inda za a kashe goma tara ba ta gyaru ba.