1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Turkiya da Nahiyar Afirka

Abdullahi Tanko BalaAugust 16, 2008

Turkiya ta ƙudiri aniyar bunkasa dangantaka da Nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/EyS7
Daya daga cikin tarukan ƙungiyar gamaiyar AfirkaHoto: AP Photo


A yayin da China da India ke faɗaɗa muradun su a ƙasashen Afirka, ita kuwa Turkiya ta ƙudiri aniya ce ta bunƙasa muámalar cuɗanni-incuɗeka da Nahiyar Afrika. Abin tambaya shine ko Turkiya zata iya cimma wannan manufa da kuma haɓaka cigaban Nahiyar ta Afirka ?

A ranar litinin ɗin nan ce dai zaá gudanar da babban taron farko na ƙawancen haɗin gwiwa tsakanin Turkiya da Afirka a birnin Istanbul. Jigon taron na kwanaki huɗu shine zumunci da ƙawance na gaskiya domin wanzuwar kyakyawar makoma a gaba. Ana sa ran halartar ɗaukacin ƙasashe 53 na Afirka. Ƙasar Turkiya wadda ta ayyana kan ta a matsayin abokiyar ƙawancen ƙungiyar gamaiyar Afirka, na fatan yin amfani da wannan taro wajen ƙarfafa dangantaka da ƙasashen na Afirka, ta kuma shirya taron ne tare da taimakon ƙungiyar gamaiyar Afirka.


Muhimman fannoni da Turkiya zata so ta nuna fice a tsakanin sauran ƙasashe sun haɗa da fannin sarrafa kayayyaki da zuba jari da fasahar ƙere-ƙere da hazaƙar ƙirƙira da fannin hada -hadar kuɗaɗe da makamashi da kuma harkokin yawon buɗe idanu.


A cewar shugaban hukumar raya cigaban dangantaka tsakanin Turkiya da ƙasashen ƙetare, Musa Kulaklikaya yace tun a shekara ta 2000 Turkiya ta fara nuna shaáwarta akan Afirka, yana mai cewa taron na Istanbul wata muhimmiyar dama ce ta bunƙasa wannan dangantaka. "Yace taron na shugabanin ƙasashe da gwamnatoci wanda kuma zai gudana daura da wasu ƙananan tarukan na mahalarta zai bada damar kyautata dangantaka tsakanin Turkiya da Afirka sannan da binciken hanyoyi ƙarin haɗin kai a tsakanin su."


A dangane da muhimmancin Afirka ga ƙasashen China da India kuwa waɗanda ke bunƙasa ta fannin tattalin arziki da cigaban masanaántu, Musa Kulaklikaya ya nuna irinin damammaki da Turkiya take da su na zuba hannun jari a ƙasashen Afirka fiye da ƙasashen na China da India. "Yace ƙasancewar a tsawon tarihi bamu da wata matsala da Afirka, kuma bama daga cikin ƙasashe waɗanda suka yi mulkin mallaka, ya sa muka shirya wannan taro domin taimakawa Afirka fita daga ƙangin matsalolin da take fama da su, ta hanyar yin amfani da Albarkatun da Allah ya hore mata a matsayin madogara, za kuma mu zauna domin duba hanyoyin da za mu haɗa hannu don cigaban tattalin arziki da kuma samar da ƙawance mai ƙarfi don bunƙasa aládu a tsakanin alúmomin mu."


Domin ƙara bunƙasa dangantakar tsakanin Turkiya da ƙasashen Afirka, maáikatar harkokin wajen Turkiya ta ƙudiri ƙara yawan ofisoshin ta na diplomasiyya a faɗin nahiyar ta Afirka, inda a yanzu zata buɗe sabbin ofisoshin jakadanci guda goma sha biyar da kuma ofishi ɗaya na ƙaramin jakada a ƙasashen na kudu da Hamadar Sahara. A saboda haka Musa Kulaklikaya yace sannu a hankali Turkiya na ƙara shiga ƙasashen Afirka. Yace sauran hukumomin Turkiya suna gudanar da harkoki a ƙasashe goma sha bakwai na Afirka, to amma da taimakon masu ruwa da tsaki, zaá ga gudunmawar Turkiya a ƙasashe fiye da Talatin a faɗin Afirka.


Manufar Turkiya na buɗe ƙofofin ta ga Afirka ya faro ne dai tun a shekarar 1998 da nufin bunƙasa dangantakar ta da ƙasashen na Afirka ta fannin siyasa, tattalin arziki da cinikayya da bunƙasa aládu. Hasali ma hakan ce tasa Turkiyan ta keɓe shekarar 2005 a matsayin shekara don cigaban Afirka.