1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakatar tattalin arziki tsakanin Amurka da Sin

July 29, 2009

Tattaunwar Amurka da Sin kan farfaɗo da tattalin arziki

https://p.dw.com/p/IzaH
Henry Kissinger da Wang QishanHoto: AP

A karshen tattaunawarsu ta kwanaki biyu a birnin washintong, magabatan Amurka da na Sin sun yi alkawarin aiki tare domin kalubalantar matsalolin tattalin arziki , makamashi, da sauyin yanayi da Duniya ke fama dasu.

Ɓangarorin biyu sun tattauna muhimman batutuwa da suka danganci yadda zasu kalubalanci manyan matsaloli da Duniya ta tsunduma. Amurka ta bayyana wa Sin matsayin ta da kuma irin bukata da take dasu na ganin cewar ta farfado da harkokin kasuwannin hada-hadanta.

A matsayin ƙasa da tattalin arzikinta ya ke cigaba da bunkasa a Duniya, Sin tana da matukar tasiri wajen farfaɗo da harkokin kasuwanci.

Sakataren kuɗi na Amurka Timothy Geithner, yana mai ra'ayin cewar hakki ya rataya a wuyan ƙasashen biyu na ceto Duniya daga cikin tattalin arziki da take ciki...

" Zamu fara wani gagarumin aiki a yau, inda zamu kafa tubalin ingantacciyar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, wanda kuma keda nufin cimma buri"

Hillary Clinton in Indien
Hillary Rodham ClintonHoto: AP

Shi kuwa mazarci kan harkokin da suka danganci yankin Asia, wanda kuma ke zama tsohon direktan harkokin yankin Asia a gwamnatin George W Bush data gabata, Dennis Wilder, yana mai ra'ayin cewar zai kasance abu mawuyaci a samu sauyin alkibla cikin gaggawa dangane da sauyin tsarin kan irin kayayyakin da za a fitar zuwa kasuwanni. Domin Sin din tayi bayanin haka a fili...

" a lokacin tattaunawar ,Sin ta tabbatar dacewar wannan babbar matsala ce data daɗe, kuma bazai kasance abu mai sauki ba ta farfado da tattalin arzimmu"

Adangane da batun sauyin yanayi kuwa, ɓangarorin biyu sun bayayana manufarsu na ganin cewa sun hada kai wajen cimma burin inganta sabbin hanyoyin samarda makamashi, da kalubalantar ɗumamar yanayi da hanyar rage hayakin da masana'antu ke fitarwa.

A ɓangaren manufofinsu na ketare kuwa, Amurka da Sin sun jaddada bukartar cigaba da inganta manufofinsu. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton tace, ana iya bayyana tattaunawar ta yini biyu da kasancewa mai haifar da ɗa mai idanu, duk kuwa da cewar an zayyana batutuwan ne, kuma daga lokaci zuwa lokaci bangarorin biyu zasu cigaba da ganawa domin bitar matsalolin..

" Clinton tace, mun tattauna batutuwa da suka shafi 'yamcin biladama masu yawa a Uigure, da halin da ake ciki a Xinjiang, inda muka bayyana damuwammu. Kuma mun yi musayar ra'ayoyi da wakilan ƙasar ta Sin dangane da manufofinsu a kanmu".

USA Finanzminister Timothy Geithner
Timothy GeithnerHoto: AP

A gunduwar Xinjiang na ƙasar ta Sin dai , an fuskanci tashe-tashen hankula a farkon watan Yuli da muke ciki, tsakanin musulmi tsiraru dake Uigure da jami'an tsaro. Rahotannin hukumomi dai sunyi nuni dacewar, rikicin yayi sanadiyyar mutuwan mutane 197.

Mataimakin Primiyan Sin Wang Qishan, ya hakikance cewar ƙasashen biyu zasu yi aiki kafaɗa da kafaɗa wajen kafa tubalin ingantaccen tattalin arziki tsakaninsu, dama Duniya baki ɗaya.

Mawallafiya: Zainab Mohammad

Edita: Umaru Aliyu