1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangata tsakanin Fransa da Jamus

Yahouza SadissouOctober 11, 2005

Makomar danganta tsakanin Fransa da Jamus bayan hawan Angeller Merkel a matsayin shugabar gwamnatin Jamus.

https://p.dw.com/p/BvYx
Hoto: dpa

Tun lokacin da shugaban gwamnatin Jamus Geher Schroder, ya bayana shirya zaben yan majalisun taraya kafafofin sadarwa a nahiyar turai, da masharahata su ka yi bayyana ra´ayoyi a game da yada dangata zata kasance tsakanin Jamus da Fransa, idan Angeller Merkell ta lashe zaben.

Bisa jagoranci Geher Schröder, Fransa da Jamus sun kasance tamkar yar juma da yar jummai, a yayin da Geher Schröder da Jacque Chirak shugaban kasar Fransa, ke matsayi Hassan da Hussaini.

Shawarwarin su da ra´ayoyin su, a mafi yawan lokatta su na kama da juna, kuma su ke tafe da akalar kunguiyar gamayya turai.

Da dama daga masu kulla da al´ammuran siyasa, na hasashen cewa, da zaran Angeller Merkel ta samu damar hawan kujerar shugaban gwamnati, zata karkata akalara dangatar Jamus wajen Britania da Amurika.

A watan July da ya gabata, Angeller Merkell, ta kai ziyara a kasar Fransa, inda ta gana da shugaban kasa Jaques Chirak ,ta kuma tabatar masa da cewa, a shire ta ke ta cigaba da huldodin diplomatia, da cude ni in cude ka, tsakanin Jamus da Fransa, idan ta samu nasara lashe zabe.

Jim kadan baya da a ka bayana sakamakon yarjenejniyar da a ka cimma tsakanin SPD da CDU a jiya talata, wace ta budewa Angeler Merkell kofar fadar shugaabn gwamnati, Jaques ya yi mata waya domintaya ta murna.

Kakakin fadar Elysee, ya sannar cewa Chirac, ya yi mata fatan alheri, a wannan saban jagoranci da ra samu, ya kuma gayyace ta, a kasar Fransa da zaren ta kama aiki, domin su duba sabin hanyoyin karfafa dangata tsakanin kasashen 2 masu fada aji a nahiyar turai.

Shugaba Jaques Chirak a cikin jawabin da ya aikwa Angeller Merkell, ya nanata da babbar murya, mahimmanci huldodi masu dogon tarihi tsakanin Fransa da Jamus,ya ce kuma ba ya da kwankwanto a game da burin da sabuwar shugabar gwamnatin ke dauke da shi,na cigaba da kara karfafa wannan dangata, don kwattata rayuwar alummomin kasshen 2, da ma na turai gaba daya.

A daya wajen kuma, Jaques Chirak yayi hira ta wayar talho ga shugaba mai barin gado Geher Schröder , inda yayi masa yabo na mussman,a game jan namijin kokarin da ya kawo, a duk tsawon mulkin sa, domin kitsa dangata inganttata, tsakanin Fransa da Jamus, da kuma hazaka da basira, da ya nuna ta fannin gina kungiyar gamaya turai, da cigaban a´lummomin ta.

Ranar juma´a mai zuwa idan Allah ya nuna mana za a shirya wata ganawa tsakanin Shirak, da Geher Schröder a cikin shirye shiryen taron koli na shuwagabanin kasashe da na gwamnatoci na kungiyar gamaya turai, da za ayi ranar 27 ga watan da mu ke ciki a birnin London.

Geher Schröder, zai wakilci Jamus a wannan taro, kasancewar Angeller Merkel, zata hau matsayin ta, na shugabar gwammnati a watan november.

A nasu bangare, Jaridu a kasar Fransa, a yau sun rubuta sharhuna iri iri ,a game da sabon shafin gangata da ya bude tsakanin Fransa da Jamus, da dama daga jaridun, sun ruwaito cewa, duk da kalamomin baka, da mahunkunta kasashe su ke yi na ci gaba da karfafa wannan dangata, cilas sai an samu yan cenje- cenje, tsakanin lokacin baya, da na yanzu kamar yada hausawan kan ce wai sarki goma zamani goma.