1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangataka ta yi tsami tsakanin Girka da Ostriya

Gazali Abdou TasawaFebruary 26, 2016

A wani abin da ke zama karuwar gurbacewar dangantaka tsakanin Kasashen Girka da na Ostriya kan batun 'yan gudun hijira, kasar Girka ta yi watsi da tayin ministan cikin gida na Ostriyar na kai wata ziyara a Girkar.

https://p.dw.com/p/1I2w3
Westbalkan Konferenz Sebastian Kurz Johanna Mikl-Leitner Wien Österreich
Hoto: Getty Images/AFP/H.Fohringer

A wani abin da ke zama karuwar gurbacewar dangantaka tsakanin Kasashen Girka da na Ostriya kan batun 'yan gudun hijira, Kasar Girka ta yi watsi da tayin ministan cikin gida na kasar Ostriyar Johanna Mikl-Leitner na kawo ziyara a kasar ta Girka.

A wani mataki na nuna adawarta da matakin Kasar Ostriya na shirya wani taron kasashen yankin Balkan kan batun 'yan gudun hijira ba tare da gayyatarta ba, Kasar Girka ta gayyaci jakadanta na birnin Vienne zuwa gida domin tattaunawa.