1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

071108 Pogromnacht

Graupner, Hardy November 11, 2008

A halin da ake ciki yanzu ta´asar da aka ƙaddamar kan Yahudawa a nan Jamus a daren tara zuwa 10 ga watan Nuwanban shekarar 1938 na gushewa daga zukatan ´yan ƙasar musamman ma dai matasa.

https://p.dw.com/p/FrcN
Shugabar gamaiyar Yahudawa a Berlin, Lala Sueskind, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugabar majalisar tsakiya ta Yahudawa a Jamus, Charlotte Knobloch, a gun bukin tunawa da zagayowar shekaru 70 da ta´asar da aka yi Yahudawa a JamusHoto: AP

A halin da ake ciki yanzu ta´asar da aka ƙaddamar kan Yahudawa a nan Jamus a daren tara zuwa 10 ga watan Nuwanban shekarar 1938 na gushewa daga zukatan ´yan ƙasar musamman ma dai matasa. To ko shin wasu irin abubuwa na zamani ya kamata a yi na tunawa da wannan tarihi domin bawa matasan damar gane wannan ɓangare na tarihin Jamus? Shirin Mu kewaya Turai na wannan makon zai duba ƙoƙarin da shugabannin wannan ƙasa ke yi ne na amfani da wannan ɓangare na tarihin ƙasar domin kaucewa sake aukuwarsa nan gaba.

Hare-hare na ƙyamar Yahudawa a Jamus wanda gwamnatin ´yan Nazi ta bayyana shi da Kristallnacht ko dare mai ƙyalli yanzu ya cika shekaru 70 da aukuwa. Kamar a kowace shekara a daidai wannan lokaci a bana ma shugabannin siyasa a Jamus da cibiyoyin Yahudawa da sauran al´umomin Yahudawa a nan ƙasar sun yi gudanar da zaman juyayi don tunawa da wannan ta´asar da ta auku daga daren tara zuwa 10 ga watan Nuwanban shekara ta 1938, inda ´yan bangan gwamnatin ´yan Nazi suka kai hare hare tare da ƙona kantuna da wuraren ibadar Yahudawa da cin zarafinsu. To sai dai duk wasu jawabai daga shugabannin siyasa ba za su yi wani tasiri na a zo a gani ba wajen faɗakar da matasan wannan zamani don ka da su yi fatali da wannan abin tarihi. Inge Lammel Bayahudiyar Jamus ta shaida wannan daren na ta´asar da Jamusawa ke kira wai daren Pogrom a birnin Berlin sannan ta na ´yar yarinya.

“Sun lalata wuraren ibadarmu sun cunna musu wuta. Sun lalata gidaje da kantuna kana sun yiwa mutane kisan gilla. Lalle wani mummunan hali ne aka shiga ciki a wancan lokaci. A lokacin da na je gida da daddare mahaifiyata ta faɗa mun cewa an yi awon gaba da mahaifina zuwa sansanin gwale-gwale. An sako shi bayan makonni shida. Ta faɗawa mahaifina da ya gaggauta ficewa daga Jamus tare iyalinsa in ba haka ba za a sake kawo mana wannan hari.”

Inge Lammel na ɗaya daga cikin mutanen da ba za su taɓa mancewa da hare-haren ƙyamar Yahudawa a shekarar 1938 ba. To sai dai ga wasu Jamusawa musamman matasa wannan abun da ya faru a zamanin baya ba dole ne a riƙa tunawa da shi ba.

“Me ka ce? Tara ga watan Nuwanba? Bani da wata masaniya game da abin da ya faru.”

To ke fa?

“Wallahi ni ma ban san komai game da wannan rana ba.”

Waɗannan Jamusawan ma´aurata biyu da aka yi kaciɓis da su a cikin garin Berlin da ma wasu dake wucewa sun nuna tababa game da daren da aka aikata ta´asar akan Yahudawa. To amma wasu ´yan makaranta dake ziyarar buɗe ido a babban birnin na Jamus na da masaniya ga wannan daren wanda Jamusawa ke yiwa laƙabi da daren Pogrom.

“Ranar da aka fara fatattakar Yahudawa.”

“E, alal misali a cikin darasin tarihin daular ´yan Nazi, a wannan dare aka ƙaddamar da hare hare da cunna wuta a kantunan Yahudawa da wuraren ibadarsu da lalata sauran cibiyoyin Yahudawa.”

“An aikata wannan ta´asar a faɗin daular ta Jamus amma ta fi yin muni a nan Berlin.”

Ko shakka babu masana tarihi ka iya saka ayar tambaya da cewa ko wannan lamarin ya fi yin muni a Berlin, to amma haka ´yan makaranta suka koya a darussa game da abubuwan da suka wakana a shekarar 1938. To sai dai Kathrin Meyer ta cibiyar ƙasa da ƙasa ta nazarin kisan ƙare dangin da aka yiwa Yahudawa dake a Berlin ta san cewa sau da yawa ba a bawa wannan batun muhimmancin da ya kamata musamman a makarantu.

“Idan wannan batun ya tsaya a cikin darasin tarihi, to ga mai shekaru 15 a yanzu zai ga abin kamar ya auku ne a zamanin kakannin kakanni. Yanzu ƙasashe kusan 10 sun fara wani shiri tsakaninsu na tattara bayanai game da aƙidar ƙyamar Yahudawa. Da farko bayanan sun ƙunshi dukkan nau´o´i na ƙyamar baƙi da wariyar jinsi kamar yadda ake gani a cikin makarantunmu na yanzu da suka haɗa dukkan jinsuna da al´ummomi daban daban. A cikin wannan aikin an taɓo batun rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya.”

Idan ƙungiyoyin mawaƙa kamar ƙungiyar mawaƙa ta birnin Kolon suka rera waƙoƙi game da ta´asar ta daren Pogrom da nuna manufar ƙyamar Yahudawa a tsakanin Jamsuwan wancan lokaci da na yanzu to hakan ya fi yin tasiri a rayuwar matasan fiye da darussan tarihi a makarantu. Sai fa idan za a shigar da matasan ne a ayyukan bincike waɗanda za su ba su damar sanin ainihin abubuwan da suka wakana a wancan lokaci. Wata makaranta dake birnin Bielefeld ta samu nasarar gudanar da wannan aikin binciken inda ´yan makarantar da kansu suka gudanar da bincike kan abin da ya faru ga Yahudawa a shekarar 1938.

Wani malami a makarantar ya ce kuskure ne a ce wai matasan na yau ba su da sha´awar sanin ta´asar da aka aikata kan Yahudawa.

“Dole ne a riƙa ba su labarin wannan tarihi. Suna sha´awar jin wannan labari idan aka bi hanyoyin da suka dace. Har yanzu akwai wurare da yawa a Berlin da ya kamata a nuna musu. Babu wahala idan kana zaune a Berlin.”

To sai dai abin baƙin ciki shi ne har yanzu ana aikata ba daidai ba akan Yahudawa. Alal misali a ´yan kwanakin da suka wuce an kaiwa wani rukunin Limaman Yahudawa hari a Berlin inda aka ci musu mutunci. Sannan a birnin Hamburg an kai hare hare a wata maƙabartar Yahudawa inda suka lalata ta. A watannin shidan farko na wannan shekarar alal misali ´yan sanda sun yi rajistar laifuka irin na ƙyamar Yahudawa fiye da 500 a faɗin Jamus.

Ud Joffe shahararren mawaƙi Bayahude mazauni a birnin Berlin na mai ra´ayin cewa kamata ya yi a ƙara nunawa matasa asarar da Jamus ta yi sakamakon kisan ƙare dangi sannu a hankali da aka yiwa Yahudawa a zaman mulkin ´yan Nazi.

“A nuna musu abin da ba su sani ba domin ta haka matasan za su samu wata dangantaka game da abubuwan da suka wakana a da. Na san za su yi mamakin aukuwar wannan ta´asa.”