1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daruruwan mutane sun halaka a hargitsin kasar Iraqi

Hauwa Abubakar AjejeAugust 31, 2005

Kimanin mutane 650 suka rasa rayukansu a lokacinda aka firgita yan shia dake bikin tunawa da shahadar sheikh Musa Khadim a birnin Bagadaza

https://p.dw.com/p/Bva4
Takalman wadanda suka fada cikin ruwa a bakin kogin Tigris
Takalman wadanda suka fada cikin ruwa a bakin kogin TigrisHoto: AP

Jami'an asibiti sun baiyana cewa yawancin wadanda suka rasa rayukan nasu mata ne da yara kanana da kuma tsofaffi.

Wannan dai shine hasarar rayuka mafi muni da aka taba yi a Iraqi tun lokacinda Amurka ta kaddamar da yaki akan Iraqi shekaru biyu da suka shige.

Yawancin wadanda suka mutun sun fada ne cikin kogin Tigris a lokacinda aka tsorata gun gun yan shia da suke kan hanyar su ta zuwa bikin tunawa da shahadar Musa Khadim wani shugaban shia,inda wani yayi shelar cewa akwai dan kunar bakin wake tsakaninsu.

Wani jami'in tsaro yace ya zuwa lokacin wannan rahoto an gano gawarwakin mutane 647 wasu 301 suka samu rauni yayinda kuma ake ci gaba da nemo wasu gawarwakin daga cikin kogin.

Wasu mutane 7 kuma sun rasa rayukansu a wani harin na daban da wasu yan bindiga suka kai akan wasu yan shi'a dake kan hanyarsu ta zuwa birnin Bagadaza daga Kadhimiya domin halartar wannan biki na tunawa da Musa Khadim.

Wadannan balao'in su zone a dai dai lokacinda ake kai ruwa rana game da kundin tsarin mulkin kasar wanda yan sunni suke kokarin ganin an ki amincewa da shi a lokacin kuri'ar raba gardama da za'ayi ranar 15 ga watan oktoba.

Jakadan kasar Amurka a Iraqi Zalmay Khalilzad ya baiyanawa manema labarai cewa daftarin tsarin mulkin da aka mikawa majalisa a ranar lahadi bayan an kwashe makonni uku ana tafka muhawara akansa,har yanzu bai kammala ba, tunda a cewarsa yan Iraqin su kansu da ma yan majalisa sun kasa gudanar da gyare gyare da suka kamata cikinsa.

A yanzu dai shugabanin yan sunni da suke neman goyon bayan alummomin kasar sun ce zasu tattauna da Muqtada As Sadr,wanda shima baya goyon bayan sabon kundin tsarin mulkin da aka tsara shi karkashin jagorancin Amurka.

Muqtada as Sadr yana da goyon bayan yawancin jamaar Iraqi musamman saboda gwagwarmaya da yake yi game da mamayar Amurka.

A halin yanzu dai shugaba Ibrahim al Ja'afari ya ya bayarda hutun kwanaki uku na zaman makoki domin nuna alhini ga wadanda wannan masifa ta rutsa da su.