1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daurin rai da rai ga Mugesera a Ruwanda

Salissou BoukariApril 15, 2016

Wata kotu a birnin Kigali na kasar Ruwanda ta kama Leon Mugeresa da laifin tunzura jama'a wajen kisan kare dangi da ya gudana a shekarar 1994 kan 'yan kabilar Tutsi.

https://p.dw.com/p/1IWnK
UN-Tribunal in Tansania gegen mutmaßliche Ruanda Kriegsverbrecher
Hoto: picture-alliance/dpa

Shi dai Léon Mugesera daya ne daga cikin tsofaffin kusoshin jam'iyyar tsohon shugaban kasar marigayi Juvenal Habiyarimana. An yanke masa daurin rai da rai, bisa kamashi da laifin ingiza mutane ga yin kisan gilla a lokacin yakin basasan da ya barke a 1994 a kasar ta Ruwanda inda 'yan kabilar Hutu suka yi ta karkashe 'yan Tutsi.

A shekarar 2012 ne dai kasar Kanada ta tasa keyar Mugeresa zuwa kasar ta Ruwanda, kuma alkali Antoine Muhima na kotun kasar ya ce ta kotu ta kama shi da laifin gama baki da wadanda suka aikata kisan gilla na kare dangi ga 'yan kabilar ta Tutsi. Sai dai tuni Mista Mugeresa ya daukaka karan wannan hukunci, inda ya ce ko da aka yi wannan aika-aika, shi ya na kasar Kanada.

Alkallan dai sun zargeshi da laifin yin wani jawabi na nuna kyamar 'yan kabilar ta tutsi a shekarar 1992 a yankin Yammacin kasar ta Ruwanda yayin wani taron gangamin jam'iyyarsa, kuma alkalai sun ce wannan jawabi da ya yi na daya daga cikin abin da ya rura wutar rikicin da ma kashe-kashen da aka fuskanta.