1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Davos: Neman mafita kan tattalin arziki

Zainab Mohammed Abubakar
January 24, 2018

Shugabannin kasashe da masu fada a ji a fannin kasuwanci na ci gaba da laluben mafita a babban taron tattalin arziki na duniya da ke gudana a birnin Davos, dangane da cimma cudanya ta bai daya.

https://p.dw.com/p/2rRTZ
Davos Weltwirtschaftsforum
Babban zaman taro kan tattalin arziki karo na 48 na birnin DavosHoto: World Economic Forum/J. Polacsek

An samun ingantaccen ci-gaba a fannin tattalin arziki na duniya, a cewar alkaluman asusun lamuni ta duniya wato IMF. Wannan dai batu ne da ya dace a ce an yi marhabin dashi. Sai dai shugabar asusun Christine  Largarde ta nuna ba haka lamarin yake ba inda ta ce: "Bunkasar tattalinlin arziki batu ne da ya dace a gani tun daga cikin gida, ba a matakin kasa da kasa kadai ba kamar yadda ya kasance a shekaru gomma da suka gabata, amma cikin kasashen".

Schweiz Davos IWF Chefin Lagarde
Shugabar Asusun IMF Christine Lagarde Hoto: Reuters/D. Balibouse

Shugabannin manya kungiyoyin kasuwanci, da jiga-jigai a fannin kudi da shugabannin siyasa sun cimma yarjejeniyar bude kan iyakokin kasashe don shigara da hajoji, da ayyuka har da ma kudade, a wani mataki da suka kira samar da yanayi mai inganci a duniya. Sai dai a zauren babban taron na bana wanda shi ne karo na 48, wakilai na dasa ayar tambaya dangane da yadda za'a warware matsalar cudanyar kasuwancin bai daya ta hanyar samar da adalci, a daya hannun kuma za'a iya iya kare tsari na jari hujja daga nata akidun.

Manyan misalai biyu su ne ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai da zaben Donald Trump a matsayin shugaban Amurka. Maurice Obstfield, jami'in tattali a asusun bada lamuni na duniya IMF cewa ya yi: "Masu kada kuri'a a kasashen da suka cigaba a fannin tattalin arziki na da shakku kan hukumomin siyasa, dangane da ko zasu iya cimma tudun dafawa a fannin tattalin arzikin kasa".

Schweiz Davos - Indiens Premierminister Narendra Modi beim World Economics Forum (WEF)
Firaministan kasar Indiya Narendra Modi Hoto: Reuters/D. Balibouse

Framinista Narendra Modi na Indiya, kasar da ke zama ta biyu mafi karfin arziki a yankin Asiya, ya yi kokarin kare cudanya ta bai daya a jawabinsa na bude taron tattalin arzikin na Davos, sai dai shi da kansa ya yi amannar cewar, a zahirin gaskiya, kolliya bata biyan kudin sabulu ba. Shugaban kasar Switzerland Alain Berset, da ya yi jawabi kafin Modi, ya hakikance cewar, ko tunanin cewar matsayin kasuwanni ne zasu daidaita komai, labari ne na kanzon kurege kawai inda ya ce: "A cikin shekaru gommai da suka gabata, walwalar kasashe da matsayin tattalin arziki sun sha karo da juna. Hakan bai dace ba, kazalika hasashen yiwuwar hakan".

A yayin da murya ta zo daya tsakanin maharta babban taron tattalin arzikin na Davos kan bukatar samar da mafita kan irin wannan rashin daidaito, akwai sabanin ra'ayi dangane da takamamme yadda hakan zai tabbata.