1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

De Mistura ya bukaci kawo karshen rikicin Siriya

Abdul-raheem Hassan
October 7, 2016

Wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Staffan de Mistura, ya yi kakkausar suka kan yadda ake ci gaba da luguden wuta akan fararen hula a gabashin Aleppo.

https://p.dw.com/p/2Qzbr
Schweiz Genf Staffan de Mistura press conference
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Trezzini

De Mistura ya kuma ce gwamnatin Siriya na shirin sauya dabarun yaki na samun goyon baya mai karfin gaske daga kasar Rasha, domin ganin sun karbe dukkanin yankunan da ke hannun 'yan tawayen nan da karshen wannan shekara, a saboda haka ya ke kira ga 'yan tawayen da su fice da ga yankunan da suke. Rayuwar fararen hula akalla 277 dai na cikin mawuyacin hali a gabashin birnin na Aleppo.

Shi ma dai shugaban kasar Siriyan Bashar al-Assad, jaddada kudirinsa na ganin ya maida yankunan da ke hannun 'yan tawayen izuwa karkashin ikon gwamnati ya yi, yana mai cewa ba zasu zuba ido 'yan ta'adda su mamame ko ina a kasar ba, a dangane da haka ya zama wajibi su dauki dukkanin matakan da su ka dace na kakkabe 'yan tawaye nan ba da jimawa.