1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dimokradiyya ta kan kama a Afghanistan inji..

March 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6L

Shugaba Bush na Amurka ya yaba a game da yadda mulkin dimokradiyya ya kankama a kasar Afgahanistan.

Mr Bush , wanda ya fadi hakan a dazu dazun nan a taron manema labarai daya gudanar tare da shugaba Hamid Kharzai, ya tabbatar da cewa ci gaban mulkin dimokradiya da kasar ta dasa danba a kansa ka iya zama abin koyi ga sauran kasashe na duniya.

Shugaban na Amurka, wanda ya kai ziyarar ba zata a kasar ta Afghanistan, akan hanyar sa ta fara ziyarar aiki´izuwa India da Pakistan, ya tabbatar da cewa a kwana a tashi zasu cafke madugun kungiyyar Alqeda, wato Usama Bin Laden, da suka dade suna nema ruwa a jallo.

A lokacin ziyarar tasa izuwa India, ana sa ran shugaba Bush zai gana da Firimiyan kasar, wato Manmohan Singh, game da batu daya shafi nukiliya.

Ya zuwa yanzu dai rahotanni daga India na nuni da cewa dubbannin mutane ne ke gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da wannan ziyara da shugaban na Amurka zai kai izuwa kasar a yau din nan.