1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Direbobin sun shiga yajin aiki a Kamaru

January 12, 2006
https://p.dw.com/p/BvCa

Kungiyar derebobin manyan motoci ta kamaru ta shiga cikin yajin aiki na sai baba ta gani da aka fara jiya ,wanda ya munanta halin rashin ababen hawa a cibiyoyin kasuwanci,da kuma tilastawa sojoji jigilar man fetur a fadin kasar kasar.

Kungiyar maaikatan sufuri a jiya ta fara yajin aiki akan karin haraji da kusan dala 184 akan manyan motoci da kuma karbar hanci daga jamian tsaro na kasar.

Babban birnin kasuwanci na Doula yana daya daga cikin wuraren da abin yafi muni,inda direbobin tasi suka tsauwala kudaden da suke karba hannun fasinja.

Kusan rabi daga cikin yawan jamaar kamaru miliyan 16 suna cikin kangin talauci duk da yar kwarya kwaryar masaantar mai da albarkatun koko da auduga da kofi da take da su.