1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar hana shan tana sigari a bainar jama´a fara aiki a Jamus

September 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuCg

A yau daya ga watan satumba dokar da ta haramta shan tabar sigari cikin motocin safa safa na gwamnati da cikin gine gine hukuma ta fara aiki a nan Jamus. Dokar ta kare lafiyar wadanda ba sa shan taba, amma suke shakar hayakinta daga masu sha, ta kuma hana sayarwa matasa ´yan kasa da shekaru 18 taba tare da shan tabar a bainar jama´a.