1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar haramta amfani da Nikabi ta samu karbuwa a Faransa

September 15, 2010

'Yan majalisa 246 suka amince da haramta amfani da Nikabi

https://p.dw.com/p/PCHy
Hoto: AP

A Faransa, 'yan majalisar ƙasar sun kaɗa kuri'ar haramta amfani da mayafin nan da mata musulmi ke rufe jiki gaba daya da ake kira Burqa ko kuma Nikabi. An cimma amincewa da wannan doka ne da kuri'u 246 inda ɗan majalisa guda daya kachal yayi adawa. Ana saran cewar nan da watanni shida masu gabatowa dokar zata fara aiki, idan har alkalan kotunan kasar basu yi adawa ba. Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransan dai ya gabatar da wannan shirin doka ne, a matsayin abunda ya ce danniya da nuna wariya. Dukkan macen da aka kama tana sanye da Niqabi, za ta biya tarar Euro 150 .Ayayinda mazan dake tilastawa matansu sanya shi za su biyaa euro dubu 30 tare da zaman gidan Yari na shekara guda.'Yan adawa dai sun bayyana cewa wannan dokar ta saɓawa dokokin Faransa da ma na Turai. A yanzu haka dai kasashe kamar Belgium, Spain, da wasu yankunan Italiya na la'akari da ɗaukar matakai makamacin na Faransa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar Edita: Umaru Aliyu