1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar izinin zama ga yan cirani a Amurka

May 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuLM

Shugaban Amurka George W Bush da yan majalisar dattijan Amurka sun amince da wani gagarumin shiri na dokar shige da fice wadda za ta baiwa baƙi yan cirani su kimanin miliyan 12 dake zaune a Amurka damar samun cikakkun takardun izinin zama. Matakin zai kuma ɗage takunkumin da aka sanya ta tsawon shekaru 22 wadda ta haifar da nawa ga duba buƙatun mutane kusan miliyan huɗu waɗanda ke neman izinin zama yan ƙasa na dundundun. A karon farko shirin zai baiwa waɗanda basu da takardun zaman sukunin zama a cikin ƙasar ta Amurka matuƙar sun cika dukkan sharuɗan da ake buƙata a gare su, tare kuma da biyan kuɗi dala 5,000. Bugu da ƙari dubban yan ƙasashen ƙetare na iya shiga Amurkan domin yin aiki na wucin gadi.