1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Trump da Hillary Clinton sun yi nasara

Suleiman Babayo/USUMarch 2, 2016

Zaben tantance 'yan takaran shugabancin Amirka daga manyan jam'iyyun kasar ya gudana a fiye da jihohi 10 karkashin taken Super Tuesday.

https://p.dw.com/p/1I5g6
USA Vorwahlen Bildkombo Donald Trump Hillary Clinton
Hoto: Reuters/D. Becker/N. Wiechec

Bayan kusan kammala kidaya kuri'u a zaben fitar da gwani na manyan jam'iyyun siyasa na kasar Republican da Democrat, a zaben Super Tuesday. A jam'iyyar Republican Donald Trump ke kan gaba inda ya lashe jihohi 7, sannan Ted Cruz ya samu jihohi biyu, yayin da Marco Rubio ke da jiha daya kacal, yayin da ake dakon sauran jihohi biyu. A bangaren jam'iyyar Democrat Hillary Clinton tana kan gaba a jihohi 7, yayin da Bernie Sanders yake kan gaba a jihohi 4.

Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat ga abin da take cewa. "Wannan shi ya sa nake da imanin cewa idan muka jajirce, daga masu neman rarraba mu, muka hada kai tare za mu mayar da wannan kasa ta yi aiki ga kowa."

Jam'iyyar Democrat ta yi zaben fitar da gwanin na ranar Talata da ta gabata a jihohi 11, kafin lokacin an yi a jihohi hudu. Babban mai hamayya da Clinton a jam'iyyar Barnie Sanders ya ce har yanzu akwai sauran aiki, domin yanzu haka an yi zaben fitar da gwanin a jihohi 15 saura 35, kasancewar kasar ta Amirka tana da jihohi 50. Sanders ya kara da cewa.

"Haka yana nufin abu mai yawa a gare ni, domin mutanen da nafi sani, suke sanni kafin na lashe zaben magajin gari, suka sanni kafin zama dan majalisa, kuma kafin zama dan majalisar dattawa, suke goyon baya na domin karbar madafun iko a fadar mulki ta White House."

Shi ma Donald Trump na jam'iyyar Republican yana cewa "Wannan yammaci ne na musamman. Mun riga mun samu jihohi biyar, kuma akwai yuwuwar samun kari zuwa jihohi 6, ko 7 ko 8, ko kuma 9."

Marco Rubio da ke matsayi na uku bisa samakaon zaben jam'iyyar ta Republican, ya ce babu gudu babu ja-da baya. "Wannan lokaci mai tsauri, mutane da dama suna gwagwarmaya, na san mafi yawa kuna gwagwarmaya. Kar a mika wuya ga tsoro, ko bacin rai, kar a mika wuya ga masu neman amfani da halin da kuke ciki."

Zaben na wannan Talata yana da muhimmancin gaske, domin yana zama rana guda da aka zabi wakilan masu yawa fiye da kov wace rana da ake zaben fitar da gwani, don tantance 'yan takara biyu da za su fafata a zaben kasa baki daya. Zaben da zai gudana a ranar takwas ga watan Nowamba mai zuwa, Inda za san wanda zai gaji kujerar mulki daga hannun Shugaba Barack Obama. Cikin watanni masu zuwa kowace jam'iyya za ta tabbatar da wanda ya lashe zaben fitar da gwanin.

USA Vorwahlen Kaffeetassen von Hillary Clinton und Donald Trump
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/C. Kaster