1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dortmund ta kori mai horas da 'yan wasanta

Gazali Abdou Tasawa
December 10, 2017

Kungiyar kwallon kafa ta Dortmund ta kasar Jamus ta kori mai horas da 'yan wasanta Peter Bosz a wannan Lahadi biyo bayan kashin da ta sha a gida a jiya Asabar a gaban Kungiyar Werder Breme.

https://p.dw.com/p/2p6OV
Fußball Trainer Peter Bosz
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Thissen

Kungiyar kwallon kafa ta Dortmund ta kasar Jamus ta kori mai horas da 'yan wasanta Peter Bosz a wannan Lahadi tare da maye gurbinsa da Peter Stöger tsohon mai horas da 'yan wasan Kungiyar Köln wanda kungiyarsa ta kora a makon da ya gabata. 

Shugaban kungiyar Hans-Joachim Watzke ne ya sanar da hakan jim kadan bayan wani taron gaggawa da kungiyar ta kira a wannan Lahadi. Wannan mataki ya zo ne kwana daya bayan kashin da kungiyar ta Dortmund ta sha a gida da ci biyu da daya a jiya Asabar a gaban Kungiyar Werder Brem wacce ke a matsayin ta 17 a tebirin Bundesliga. 

Bayan wasannin mako na 15 na Bundesliga, Kungiyar Dortmund wacce ta sha lashe gasar ta Bundesliga da daukar kofin zakarun Turai a shekarun baya na a matsayin ta bakwai a halin yanzu da maki 22 kacal a tebirin na Bundeliga. 

Nadin Peter Stöger sabon mai horas da 'yan wasan Kungiyar ta Dortmund ya zo ne mako daya bayan da Kungiyar Köln ta sallama shi a bisa rashin kyakyawan sakamako inda kungiyar ta kasance a matsayin ta karshe a tebirin na Bundesliga da maki uku kawai bayan wasanni 14.