1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DRC: Shugaba Kabila ya nada sabon firaminista

Gazali Abdou Tasawa
April 8, 2017

'Yan adawa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango sun yi watsi da matakin Shugaba Kabila na nada Bruno Tshibala wani dan adawa mai shekaru 61 a matsayin sabon firaministan kasar.

https://p.dw.com/p/2auiX
DRCONGO-POLITICS-KABILA
Hoto: Getty Images/AFP/J. D. Kannah

A Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango Shugaba Kabila ya nada Bruno Tshibala wani dan adawar a matsayin sabon firaministan kasar. Tshibala dan shekaru 61 a duniya na daya daga cikin abokanin gwagwarmayar Etienne Tshisekedi tsohon madugun 'yan adawar kasar da Allah ya yi wa rassuwa a ranar daya ga watan Febrairun wannan shekara. 

A watan Febrairun da ya gabata sai da jam'iyyar UDPS ta Tshisekedi ta kore shi bayan da ya nuna rashin amincewarsa da matakin nada Felix Tshisekedi da ga Etiennen Tshisekedi  kan shugabancin jam'iyyar bayan rasuwar mahaifinsa. Yarjejeniyar da aka cimma a ranar 31 ga watan Disembar da ya abata tsakanin bangaren masu mulki da kuma 'yan adawar kasar ta Kwango ce ta tanadi mika mukamin firaministan ga 'yan adawa. 

A yanzu dai ana kyautata zaton nadin firaministan Bruno Tshibala zai ya kawo karshen danbarwar siyasar da ta dabaibaye kasar tun bayan Shugaba Kabila ya ki mika mulki bayan da wa'adin mulkinsa ya kawo karshe a ranar 20 ga watan Disamban da ya gabata.