1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DRC: Yajin aikin nuna adawa da tazarcen Kabila

October 19, 2016

A Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango Jama´a sun karba kiran 'yan adawa na kaurace wa wuraren aikinsu domin nuna rashin amincewarsu da yinkurin Shugaba Joseph Kabila na yin tazarce  kan karagar mulkin kasar

https://p.dw.com/p/2RRUw
DR Kongo Streik Archivbild
Hoto: Getty Images/J.Kannah

Wannan ya biyo bayan matakin kotun tsarin mulkin kasar na amincewa da dage zabukan kasar har ya zuwa shekara ta 2018, wnnan kuwa duk da cewa wa'adin mulkin da kundin tsarin mulkin kasar ya halitta wa Shugaba Kabila zai kawo karshen a watan Disamba mai zuwa.

'Yan adawar kasar sun yi kiran da a bijire wa yunkurin Shugaba Joseph Kabila na kin shirya zabe da kuma cigaba da kasancewa kan karagar mulkin Jamuhuriyar Demokadiyar Kwango har zuwa shekara ta 2018. Cimma matsayar gudanar da zaben a shekarar 2018 ya zo ne a lokacin da tarayyar turai ta yi barazanar kakaba wa kasar takunkumi. A wani mazaunin Kinshasa babban birnin kasar Charles Kabulo yayi bayani game da halin da kasar da fada ciki:

"Masu mulkin yanzu ba sa son kawo sauyi ko inganta lamurra, domin wannan mataki na yajin aiki na gama gari ba karamin koma baya ne idan ba haka ba ta ya ya kake fassara yadda mutanen da aka yiwa albashi amma sun amince da kauracewa wuraren aikinsu.Wannan na nufin sun kosa ne da halin da ake ciki" 

Joseph Kabila Präsident Demokratische Republik Kongo
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler


A farkon wannan mako ne dai Kotun tsarin mulkin kasar ta Kwango ta amince da dage zaben kasar zuwa watan Apirilun shekara ta 2018 a maimakon 27 ga watan gobe da jadawalin farko ya tsayar. Ranar Litinin Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta tura daruruwan dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa Gabashin kasar domin dakile dukkan wani rikici da ka iya barkewa saboda dage zaben da kotu ta yi.

To sai dai kuma babbar jam'iyyar adawa ta UDPS ta sa kafa ta yi fatali da wannan hukunci inda ta yi kiran da jama'a su shiga zang-zanga. A makon jiya ne jakadan Majalisar Dinkin Duniya a jamhuriyar demokaridiyar Kwango, Maman Sambo Sidikou ya yi gargadin cewa kasar na iya fadawa rikicin siyasa muddin ba'a yi wa tifkar hanci ba. Itama a nata bangaren Mama Lipasa wadda ke zaune a Kinshasa ta bayyana bukatar shugabannin siyasa su yi kokarin tabbatar da hadin kan al'ummar kasar domin dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali:

Kongo Demonstration der Opposition in Kinshasa
Hoto: Getty Images/AFP/E. Soteras


"Ina ganin wannan matsalar da muke fuskanta tana bukatar shugabannin siyasa su hada kansu, al´umma suna kokawa koyaushe hakan babu dadi, muddin muna son kaucewa zubar da jini to dole a hada kan jama´a"
 

Kasuwanni da shaguna sun kasance a rufe yayin da jama'a a wasu garuruwan suka yi zamansu a gida don gudun abin da ka je ya zo. Hukumomi sun aike da soji zuwa gine-ginen gwamnati da majalisar dokoki. An kuma rawaito cewa da dama harkokin kasuwanci ba sa tafiya yadda ya kamata, gidajen mai da dama sun kasance a rufe.