1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban mutane Boko Haram ta raba da muhallansu

Kamaluddeen SaniSeptember 4, 2015

Sama da mutane miliyan daya da dubu dari ne aka lalata musu gidaje a Arewacin Najeriya tun lokacin da kungiyar Boko Haram ta fara kaddamar da kai hare hare.

https://p.dw.com/p/1GRPl
Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
'Yan gudun hijira a BamaHoto: Reuters/S.Ini

Wata Cibiya mai suna Thomas Reuters Foundation da ke tallafawa wadanda yaki ya daidaita ta bayyana cewar rikin 'yan kungiyar Boko Haram da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ya tilasta wa mutane sama da 800,000 barin muhallan su tun a watan yuni na wannan shekarar.

Sama da mutane miliyan daya da dubu dari ne aka lalata musu gidaje a Arewacin Najeriya tun lokacin da kungiyar Boko Haram ta fara kaddamar da kai hare hare a shekara ta 2009.

Mai magana da yawun kungiyar Red Cross ta duniya Aurélie Lachant ta fada wa cibiyar Thomas Reuters cewar akwai matsalolin 'yan gudun hijira da wadanda yaki ya tilasta wa barin muhallansu masu tarin yawa ciki har da tarayyar Najeriya.

A kalla dai tara daga cikin mutane goma da yaki ya tilasta musu barin muhallansu a Najeriya na tare ne da 'yan uwa na kusa da sune ko kuma sansanin da aka tanadar don saukar mutanen da rikin Boko Haram ya dai-dai ta.