1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban mazauna a Zirin Gaza sun kwarara cikin Masar

January 23, 2008
https://p.dw.com/p/CwJK

Dubun dubatan Palasɗinawa daga Zirin Gaza sun kwarara zuwa cikin Masar bayan an fasa ramuka da dama a cikin bangon da ya raba iyakokin Gaza da Masar. Mutane sun yi ta rige-rigen sayen abinci, mai da dai sauran kayakin masarufi da suka yi ƙaranci sakamakon toshe kan iyakokin Gaza da Isra´ila ta yi. Masu tsaron kan iyakokin Masar ba su ɗauki wani mataki ba lokacin da ´yan Gazan ke kwarara suna tsallake kan iyakar. ´Yan sanda daga Gaza dake ƙarƙashin ikon Hamas su ma sun tsaya ne suna kallon abbubuwan dake wakana. Bayan kwanaki biyar da rufe dukkan hanyoyin dake shiga Gaza a jiya talata Isra´ila ta kyale an shiga da gas na girki da kuma mai ga tashar samar da wutar lantarki guda daya tilo a Gaza. Tun a ranar lahadi aka rufe tashar saboda ƙarancin mai. A kuma halin da ake ciki kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani taron gaggawa inda ya tattauna akan rikicin dake ƙara yin tsamari a Gaza.