1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban 'yan Rohingya sun tsere zuwa Bangaladash

September 5, 2017

Dubban 'yan gudun hijira na Rohingya suna shiga kasar Bangaladash sakamamkaon rikicin da ke faruwa a kasar Myanmar.

https://p.dw.com/p/2jNTR
Bangladesch Flucht der Rohingya aus Myanmar
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Armangue

Kusan 'yan kabilan Rohingya 125,000 suka tsere gudun hijira a kasar Bangaladash daga Myanmar a kasa da makonni biyu da suka gabata, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar, inda lamuran aikin agaji ke kara tabatbarewa.

'Yan Rohingya da ke zama Musulmai suna fuskantar tsangwama daga hukumomin Jihar Rakhine na Myanmar. Tun farko hukumomin Bangaladash sun tsaurara matakan tsaro kan iyaka, domin hana 'yan gudun hijira shiga, amma daga bisani gwamnatin Firaminista Sheikh Hasina ta Bangaladash ta mika kai bori ya hau, inda aka bude iyaka ga 'yan gudun hijira.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya yi tir da galazawa da tsirarun 'yan Rohingya Musulmai suke fuskanta, lokacin da ya tattauna ta wayar tarho da jagoran kasar Myanmar Aung San Suu Kyi, kuma tana ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan ta dauki matakan dakile cin zarafin da tsirarun suke ciki. Sannan Gobe Laraba ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu zai kai ziyara zuwa Bangaladash bisa lamarin na 'yan gudun hijira.