1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban yan Shia sunyi zanga zanga a Iraki

January 6, 2006
https://p.dw.com/p/BvDV

Dubban yan shia ne a yau cikin bacin rai suka gudanar da zanga zanga a garin Sadr,a game da harin daya kashe kusan mutane 200,da kuma abinda suka kira sako sako da Amurka takeyi game da daukar matakai akan sojojin sa kai yan sunni.

Masu zanga zangar sun zargi jakadan Amuraka a Iraqi Zalmay Khalizad da kuma manyan shugabannin yan sunni,musamman Saleh al Mutlaq shugaban babbar jamiyar sunni daya ye ci gaba da korafin magudi cikin zaben da aka gudanar a kasar.

Majalisar juyin juya hali ta Islama ta shirya wannan zanga zanga bayan sallar jumaa tana mai cewa zata dauki matakai akan yan sunni da suke goyon bayan sojojin sa kai,musamman bayan hare hare na kwanaki biyu da suka shige.