1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban 'yan Sudan ta Kudu ne ke tserewa saboda yunwa

Kamaluddeen SaniApril 7, 2016

Kimanin 'yan Sudan ta Kudu sama dubu 50 suka arce zuwa makwabciyar kasar Sudan tun a farkon watan Janairu, domin kaucewa rikice-rikice gami da karancin abinci.

https://p.dw.com/p/1IRS0
Sudan, Symbolbild Massenvergewaltigung
Hoto: picture-alliance/Ton Koene

Sudan Ta Kudu dai ta sami 'yancin gashin kanta ne daga Kasar Sudan ne tun a sheakara ta 2011 to amma shekaru biyu baya kasar sai ta tsunduma cikin wani sabon yakin basasa da yayi sanadiyyar mutuwar dubban fararen hulla tare da tilastawa karin wasu dubbai barin muhallan su.

Ofishin kula da harkokin ba da agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniyar ya ce a kalla kimanin 'yan Kasar Sudan Ta Kudu sama da dubu 55 suka isa yankin Darfur kana kuma tun farkon yakin basasar kasar shekaru biyu da suka gabata a gaba daya 'Yan Sudan Ta Kudu sama da dubu dari 200 suka nemi mafaka a kasar ta Sudan.