1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fitar da hayaki mai guba na karuwa a duniya

Abdourahamane Hassane
November 21, 2023

MaJalisar Dinkin Duniya ta ce duk da alkawuran siyasar da aka yi tsakanin gwamnatoci a kan yaki da sauyin yanayi har yanzu duniya na kan hanyar samun dumamar yanayi da kusan digiri uku.

https://p.dw.com/p/4ZG14
Hoto: PR-Video/dpa/picture alliance

Majalisar wacce ta gabatar da rahotonta na shekara-shekara a kan dumamar yanayin a birnin Nairobi na Kenya ta ce duniya na fuskantar babban hadari.Ta kuma ce tana da fargaba game da fitar da hayaki mai guban wanda kan iya wuce matakin  da aka cimma a yarjejeniyar yanayi Paris  a shekarara ta 2015. Yarjejeniyar ta tanadi  rage fitar da hayaki mai guba da ke gurbata muhali da akalla kashi 28 zuwa kashi 42 cikin dari a cikin shekaru goma masu zuwa. MDD ta bayyana wannan  rahoton ne kwanaki kadan gabanin taron sauyin yanayi na duniya COP28, wanda za a yi a ranar 30 ga Nuwamba a Dubai.