1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya ta yi biris da rikicin Afirka ta Tsakiya

Abdul-raheem Hassan
June 1, 2017

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Norway, ta nuna damuwa kan yadda hukumomi suka gaza kawo karshen yaki da ke halaka fararen hula a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/2dx8E
Zentralafrikanische Republik Behausung in Bangui
Hoto: DW/Z. Baddorf

Hukumar ta ce rikin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya yana cikin rikici mafi tsanani a fadin duniya da sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suka yi watsi da shi, rikicin kabilancin kasar ya jefa al'umma cikin halin rudani tun bayan samun 'yancin kai a shekara ta 1962. Kashi 35 cikin dari na al'ummar kasar ne kadai ke samun tsabtataccen ruwan sha, yayin da sauran kashi 27 ke zama a gurbataccen muhalli.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ruwaito cewa akalla 'yan kasar dubu 650,000 na gudun hijira a kasashe makwabta, tun bayan barkewar rikicin addini a shekara ta 2012, rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane. Duk da albarkatun kasa da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke da shi, amma sama da shekaru uku kenan kasar ke mataki na karshe a jerin kasashen da ba su da ci gaba.

Rahoton hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Norway, ta ce kasashen Kwango da Sudan ta Kudu da Najeriya da Sudan na cikin kasashen da ba sa samun kulawa da ya kamata daga sauran sassan duniya, na kawo karshen matsalolin tsaro da kasashen ke fama da shi.