1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dutsi mai aman wuta na Merapi a Indonisiya

November 6, 2010

Hurjin wuta da toka daga dutsin Merapi ya hallaka ɗaruruwan mutane a Indonisiya

https://p.dw.com/p/Q0We
Dutsi mai amen wuta na MerapiHoto: AP

Aƙalla mutane 200 su ka rasa rayuka, sanadiyar wutar da tsaunukan Merapi na ƙasar Indonisiya ke ci gaba da hurzawa. A ɗaya wajen kuma, ɗaruruwan wasu mutanen ke kwance asibiti dalilin ƙuna, da shaƙar toka mai guba da duwatsun ke yin hurji.

Ya zuwa yanzu, hukumomin agajin Indonisiya, sun kwashe fiye da mutane dubu 70 a yankin da bala´in ya rutsa da shi.

Masana ta fannin ilimin duwatsu masu aman wuta, sun ce akwai alamun sake fashewar wani dutsin. A baya bayan nan ƙasar Indonisiya, na fama da bala´o´i daga Indallahi.

Idan ba a manta ba, makon da ya gabata, wata mahaukaciyar guguwa tare da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya sun ɓarke, inda su ka biya da rayukan mutane 400.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal