1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DW da Channels TV sun kulla yarjejeniya

Abdul-Raheem Hassan/ MABDecember 9, 2015

Shugabanin tashoshin DW Peter Limbourg da na Channels TV John Momo na Najeriya za su mayar da hankali kan shirye-shiryen da suka Shafi alkinta muhalli.

https://p.dw.com/p/1HKQF
Vertragsunterzeichnung in Paris Peter Limbourg und John Momoh Vorsitzender Nigerian Channels TV
Hoto: DW/T.Walker

Tashar Deutsche Welle ta tarayyar Jamus ta cimma yarjejeiyar fadada mu'amalarta da tashar Channels TV a Najeriya, da zummar samar da shirin hadin gwuiwa kan al'amuran da suka shafi muhalli.

Shugaban Deutsche Welle Peter Limbourg da kuma takwaransa John Momo na Channels TV sun yi amfani da taron duniya kan sauyin yanayi da ke gudana a birnin Paris na Faransa don sa hannu kan wannan yarjejeniya da za ta fara aiki a watan Fabireru mai zuwa.

Ministar muhalli ta Najeriya Amina Mohammed da ta halarci bikin tare da takwararta ta Jamus Barbara Hendricks ta ce kafafen watsa labaran biyu za su taka rawa wajen wayar da kan al'umma kan batutuwan da suka shafi muhalli.

"Kama daga tafkin Chadi zuwa ga matsalar muhalli ta yankin Niger Delta i zuwa zaizayar kasa, akwai labaran da ke bukatar karfafa gwiwar shugabanni. Burinmu dai shi ne wadannan ayyuka su kawo ci gaba da zai taimaka wa rayuwar al'umma. Amma kuma suna bukatar a wayar musu da kai kan amfani da ke tattare da wadannan batutuwa. "