1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS na tattaunawa da Yahaya Jammeh

January 20, 2017

ECOWAS na kokari na karshe na samun sulhu domin ganin Yahya Jammey ya sauka cikin ruwan sanhi, kafin sojojin kasahen su saukeshi da karfi.

https://p.dw.com/p/2W9Gh
Gambia Krisengespräche in Banjul
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Omoboriowo

Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta dakatar da shirin tsige Yahya Jammeh da karfin tuwo har sai an kammala tattaunawar domin ba shi damar sauka daga kujerar mulkin Gambiya cikin girma da arziki. Tun ranar Alhamis ne sojojin taron dangi na ECOWAS ko CEDEAO suka kasance cikin shirin ko ta kwana a kan iyakokin Gambiya. Sai dai rashin samun izini daga magabata ya hanasu afka wa Yahya Jammeh a birnin Banjul don saukar da shi daga karagar mulki da tsinin bindiga. Hasali ma sojojin Najeriya sun yi ta yin shawagi a sararin samaniyar kasar da nufin kai sumame idan zarafi ya kama. Dama dai kasashe biyar ne suka bayar da gudunmawar sojoji ciki har da Senegal da Najeriya da Ghana da Togo da  Mali da kuma Senegal.