1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EFCC a Najeriya ta gurfanar da Sambo Dasuki a kotu

Kamaluddeen SaniDecember 14, 2015

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta maka tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki a kotu bisa zarge-zarge 19.

https://p.dw.com/p/1HNHA
Nigeria Sicherheitsberater Sambo Dasuki
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kudaden dai sun hada salwantar dala bilyan 2.1 da aka kebe domin yakar ayyukan kungiyar Boko Haram.

A yayin bayyanar sa a kotun tarayyar kasar a yau Sambo Dasuki gami da tsohon direktan kudin sa Shu'aibu Salisu dukkanin su sun musanta zarge-zargen da ake musu.

Bugu da kari a ta cewar Hukumar EFCC Shu'aibu Salisu ya bayyana karbar dala milyan 47 wadan da suke makare a cikin wasu akwatuna 11 daga babban bankin kasar tare da mika su ga Sambo Dasuki a shekarar da ta gabata.

Tun dai kama madafun ikon Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya dau alwashin yaki da cin hanci da rashawa gami da bankado almundahanar bilyoyin kudade a kasar.