1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Egeland na ziyarar yankunan Beirut da Isra’ila ta ragargaza.

July 23, 2006
https://p.dw.com/p/BupY

Babban jami’in kula da ba da taimakon agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya, Jan Egeland, ya kai ziyara a yankunan kudancin Beirut da Isra’ila ta ragargaza da bamabamai. A farkon jawabinsa bayan ziyarar, Egeland, ya ce a nasa ganin dai an yi amfani da ƙarfin soji fiye da kima a yankin, abin da ya ce ya zo daidai da aikata laifuffuka ga bil’Adama. Jami’in dai ya yi suka ga ɓangarorin da ke yaƙan junan da cewa, suna yaƙi ne da ba shi da wata ma’ana.

Ya dai bayyana fargabarsa ta cewa, yawan mutanen da yaƙin ya tilasa musu yin ƙaura daga matsugunansu, zai yi munin haɓaka. A halin yanzu dai, an ƙiyasci cewa kusan mutane rabin miliyan ne yaƙin ya mai da su maneman mafaka a cikin ƙasarsu.