1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ehud Olmert ya nemi gafara ga Palestinawa

November 9, 2006
https://p.dw.com/p/Buch

Praministan ƙasar Isra´ila, Ehud Olmert, ya nemi gafara ga shugaban hukumar Palestinawa, a sakamakon hare-haren da rundunar Isra´ila ta kai, a zirin Gaza jiya laraba, wanda kuma su ka hadasa mutuwar mutane kusan 20.

A ta bakin Olmert, dakarun Isra´ila sun kai da wannan hari cikin kuskure.

Praministan Isra´ila, ya gayyaci Mahamud Abbas, zuwa tebrin shawarwari, domin samo bakin zaren warware wannan taƙƙadama da ta ƙi ci, ta ƙi cenyewa.

Budu da ƙari, ya ce a shirye ya ke, ya yi belin wasu, daga pirsinonin Palestinu ,da Isra´ila ta kama.

Kakakin Palestinu a Majalisar Ɗinkin Dunia, Ryad Mansur ya buƙaci komitin Sulhu ya hiddo sanarwar yin Allah ga Isra´ila, sannan ya tura rundunar shiga tsakani a yankin.

A ɗaya wajen kuma, an ci gaba da ganawa, tsakanin Mahamud Abbas, da Praminista Isama´il Hanniey, da zumar girka gwamnatin riƙwan ƙwarya.