1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan ya halarci taron gangami kan yaki da ta'addanci

Salissou BoukariSeptember 20, 2015

Fiye da mutane dubu 100 ne suka hallara a birnin Istanbul na ƙasar Turkiya, cikinsu kuwa har da shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan, da kuma Firaminista Ahmet Davutoglu.

https://p.dw.com/p/1GZVs
Recep Tayyip Erdogan
Recep Tayyip ErdoganHoto: Getty Images/AFP/O. Kose

Shugaban ƙasar da sauran jama'a da suka hallara a wannan Lahadin a dandali na Yenikapi, sun yi Allah wadai da aiyyukan ta'addanci na 'yan tawayen Ƙurdawa a wannan ƙasa. Cikin jawabin da ya yi a gaban dubban jama'a, Shugaba Erdogan ya ce "babu maganar nuna wani sassauci ga 'aiyyukan ta'addanci". Haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kansu ne dai suka kira wannan taron gangamin a filin na Yenikapi, wani babban fili da ka iya ɗaukan aƙalla mutane milian ɗaya da rabi.

Sai dai tuni ake ganin wannan taron gangamin na mai kama da yaƙin neman zaɓe, ganin cewar watanni shidda ne suka rage ga zaɓen 'yan majalisun dokokin ƙasar na kafin lokaci, wanda shugaban ya kira bayan da aka kasa samun daidaito wajen kafa gwamnatin haɗaka a wannan ƙasa.