1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan ya soki lamirin kungiyar EU a cikin wani jawabi

Mohammad Nasiru Awal
March 21, 2017

Turkiyya za ta sake yin nazari kan dangantakarta da kungiyar tarayyar Turai bayan kuri'ar ranar 16 ga watan Afrilu.

https://p.dw.com/p/2ZgWj
Türkei Erdogan droht Niederland
Hoto: Getty Images/AFP/O. Kose

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wannan Talata ya ce za su sake yin nazari kan huldar dangantaku da kungiyar taryyar Turai EU, bayan an gudanar da kuri'ar raba gardama a ranar 16 ga watan Afrilu kan yi wa kundin tsarin mullin kasarsa kwaskwarima. A lokacin da yake jawabi albarkacin ranar dazuzzuka ta duniya a birnin Ankara, Erdogan ya kuma nanata kakkausar sukar da ya saba yi wa EU inda ya kira ta matattarar masu mulkin fir'aunanci da wariya.

Ya ce: "Tsawon shekaru sun yi ta tattake dukkan abubuwan da suka dora mana na ka'idojin EU. Da zarar ranar 16 ga watan Afrilu ta wuce za mu zauna kan teburin tattaunawa. Hakan ba zai ci gaba ba, za mu yi abinda ya fi dacewa ga Turkiyya."

A 'yan makonnin nan an yi samun takaddama dangane da takunkuman da Holland da Jamus suka sanya wa jami'an Turkiyya da ke yakin neman zabe a kasashen guda biyu kan kuri'ar raba gardamar da Turkiyyar za ta gudanar a ranar 16 ga watan Afrilu.