1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Eritrean zata marawa masu adawa da Ethiopia a Somalia baya

September 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuBO
Shgaban kasar Eritrea Issayas Afeworki ya yi alkawarin goyawa wani kawancen adawa da Ethiopia da shugabannin adawa na Somalia suka kafa a wannan mako a birnin Asmara. A lokaci daya kuma shuagba Issayas ya yi kashedin cewa Ethiopia, abokiyar gaba da Eritrea zata kwashi kashin ta a hannu a Somalia in da dakarun ta ke marawa gwamnati baya a yakin da take yi da ´yan tawaye. Shugaban ya kuma goyi bayan hare haren da ake kaiwa cibiyoyin gwamnati a kullum a birnin Mogadishu. A karshen wani taro na kwanaki 9 a jiya juma´a aka kafa sabuwar kungiyar kawancen sake ´yanto Somalia inda aka zabi Sheikh Sharif Sheikh Ahmad a matsayin shugaba.