1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Estoniya za ta fara amfani da kuɗin euro

May 12, 2010

Matakin Estoniya na haɗewa da ƙasashe masu amfani da takardar kuɗin euro.

https://p.dw.com/p/NMRH
Tutar ƙasar Estoniya.Hoto: DW

Hukumar zartarwa ta Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ba da goyon bayanta ga shirin ƙasar Estoniya na neman shiga sahun ƙasashe masu amfani da takardar kuɗin euro, a shekara mai zuwa. A ranar ɗaya ga watan Janairun shekara mai zuwa ne ƙasar za ta maye gurbin takardar kuɗinta na kroon da takardar kuɗin euro. Kenan Estoniya za ta zamo mamba ta 17 na rukunin ƙasahen masu amfani da kuɗin euro da aka fara amfani da shi a shekara ta 2002. Sharuɗan shiga wannan rukuni su haɗa ne da daidaita basuka da kuma sassauta matsayin tsadar rayuwa . A watan Yuli mai zuwa ne kuma ministan kuɗin Ƙungiyar Tarayyar Turai zai tabbatar da halalcin Estonia na haɗewa da ƙasashen masu amfani da kuɗin euro.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Yahouza Sadissou Madobi