1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ethiopia ta shiga ƙarni na 21

September 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuBj

Al´ ummomin Ethiopia, a ciki da wajen ƙasar, sun fara gudanar da shagulgulan shiga ƙarni na 21, gobe idan Allah ya kai mu.

Ethiopia na bin lissafin wattani banbam da sauran ƙasashen dunia,wanda yau da shekaru 7 da wattani 8, su ka shiga ƙarnin na 21.

Wannan lissafi ya samo tushe daga Sarki Jules Cesar na Roma, wanda yayi zamani shekaru 46, kamin aihuwar annabi Issa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

A cewar komitin da ke kula da shirya wannan gagaramin biki, shugabanin ƙasashen Afrika da dama sun karɓi goran gayyata, daga cikin su akwai shugaba Paul kagame na Ruanda, da Mwai Kibaki na Kenya, da Isma´il Omar Guelleh na Jibuti, da Omar El bashir na Sudan.

A bisa tsarin da aka yi, za a gabatar da jawabai daban-daban, wanda su ka haɗa da na Praminista Meles Zenawi, da kuma na shugaban komitin zartaswa na ƙungiyar taraya Afrika Alfa Omar Konare.

Za a gudanar da wannan biki a cikin tsatsauran matakan tsaro.