1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU da Kanada sun ratabba hannu kan CETA

October 30, 2016

Yarjejeniyar kasuwanci maras shinge tsakanin Kanada da Kungiyar Tarayyar Turai ta tabbata a ranar Lahadin nan bayan lokaci mai tsawo ana dako.

https://p.dw.com/p/2Ru4q
Belgien EU Kanada Gipfel
Shugaban hukumar EU Jean Claude Junker a dama da Justin Trudeau Firaministan Kanada a tsakiya da Shugaban Cibiyar Tarayyar Turai Donald Tusk a haguHoto: picture-alliance/dpa/S. Lecocq

Firaministan kasar Kanada Justin Trudeau ya gana da shugabanni daga Kungiyar Tarayyar Turai ta EU a ranar Lahadin nan inda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwanci da ake wa lakabi da CETA, da za ta yi tasiri ga mutane miliyan 500 daga Turai da miliyan 35 daga Kanada.

Shugaban majalisar Tarayyar Turai  Martin Schulz ya bayyana cewa wannan rana ce mai muhimmanci ga Turai da kuma Kanada.

"Ina ganin wannan rana ce mai alfanu ga Kungiyar Tarayyar Turai da Kanada bayan lokaci mai tsawo a wannan rana mun rattaba hannu kan yarjejeniya mai tsari na kasa da kasa, abin da zai amfani al'ummarmu a nan gaba wasu ma su yi koyi."