1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na neman shawo kan rikicin tattalin arziƙin Girka

March 25, 2010

Shugabannin ƙasashe 27 na ƙungiyar gamayyar Turai suna gudanar da taron ƙoli a Bruxelles da nufin laluɓo hanyoyin magance koma bayan tattalin arzikin Girka.

https://p.dw.com/p/McGc
Shugabannin Turai a BruxellesHoto: AP

Su dai shugabannin ƙasashen na Turai musamman ma waɗanda ke amfani da takardar kuɗi ta Euro ba su tsayar da hanya guda da za su bi don taimaka ma Girka farfaɗowa daga koma bayan arziƙin ba. Amma kuma da yawa daga cikinsu sun yi amannar cewa ɓullo da wani salo na tallafi haɗin guywa tsakanin Eu da kuma hukumomin lamini na duniya zai fi dacewa a wannan yanayi na rugujewar bankuna. Ko ita ma shugabar gwamantin Jamus, wato Angela Merkel sai da ce gaggawar taimaka ma Girka ba abu ne ba da ƙasarta da ke zama mafi ƙarfin masana´antu na Turai za ta amince da shi ba.

"Ta ce batun tallafi ga kasar Girka ba shi ya kamata mu sa a gaba ba. Da akwai bukatar cimma shawarwari game da yadda ya kamata a shawo kan wannan matsala. Ko ita ma gwamantin Girka ta nunar da cewa a yanzu ba ta bukatar taimako."

Symbolbild Haushaltsberatung Euro Münzen Staatsdefizit
EU na neman tallafa ma GirkaHoto: picture alliance / dpa

sai dai a daura da ƙasar ta Jamus, hukumar zartaswa ta ƙasashen Turai tana ganin cewa zai fi dacewa a bai wa ƙasar ta Girka bashin kuɗin ko da na Euro biliyon 300 ne, domin ta fara rufe makeken giɓin da kasafin kuɗinta ke fiskanta. A ɗaya hannun kuma ya bai wa takardar kuɗi ta Euro damar farfaɗowa a hada-hadar kasuwannin duniya. Dama shugaban hukumar zartaswa ta Eu na shirin kafa wani tsari da zai bai ma ƙasashen damar tafiya kafaɗa da kafaɗa a fannonin kimiya da fasaha, ilimi da kuma kawar da talauci. Jose Manuel Baroso ya ce haɗa ƙarfi da ƙarfe ne zai sa sauran ƙasashen kauce ma faɗawa cikin rikicin arziki.

"Ya ce muhawara game da giɓin ƙasafin kuɗin Girka da kuma kan wanda alhaki ya rataya mawa, sun nunar da cewa da akwai bukatar sabon tsari tsakanin ƙasashe masu amfani da takardar kuɗi ta Euro. A fili ya ke cewa dukkaninmu muna bukatan junanmu."

Kowacce daga cikin ƙasashen da ke amfani da takardar kuɗin ta bai ɗaya sun sha alwashin ɗaukan matakai musamma na tsuke bakin aljuhu domin ganin cewa ba su bi sahun takwrarsu ta Girka ba. Sai dai shugaban hukumar lamini ta duniya wato Dominique Strauss-Kahn ya ce shi ba abin da ya ke gani zai sa tattalon arzikin ƙasashen na Turai ya ci gaba da tsayawa da kafafunsa, illa kafa ƙwarya-ƙwaryar IMF a nahiyar ta Turai

IWF Direktor Dominique Strauss-Kahn
Dominique Strauss-Kahn na IMFHoto: picture-alliance/ dpa

" ya ce a gani na, nahiyar Turai na bukatan girka wani tsari da zai kare tattalin arzikinta daga fiskantar koma baya. Albarkantar wannan shiri da memebobin Eu za su yi ne, zai bayar da damar kauce ma faɗawa cikin abin da aka fiskanta a baya, wato rugujewar bankuna."

Shugabannin na ƙasashen 27 na nahiyar ta Turai sun kuma share fagen mahimman abubuwan da ƙasashe 20 da suka fi ci gaban masana´antu za su tattauna a taron da zai gudana nan gaba. Hakazalika sun yi waiwaye game da al´amuran da suka hana ruwa guda a taron da ya gudana a Copenhagen kan ɗumamar yanayi. Hasali ma dai, su shugabannin na Eu sun nunar da cewa gamayyar tasu na bukatan maƙudan kuɗaɗe wajen aiwatar da muradunta game da bunƙasa masana´antu da kuma alƙinta muhalli.

Mawallafi: Mohammed Awal Balarabe

Edita: Ahmed Tijjani Lawal