1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na sake nazarin makomar baki

Yusuf BalaOctober 7, 2015

A ranar Alhamis ne dai ministoci da ke kula da 'yan gudun hijira daga kasashen na EU za su zauna a kasar Luxembourg kan wannan shiri.

https://p.dw.com/p/1Gk9m
Luxemburg EU-Außenministertreffen Frank-Walter Steinmeier
Jami'ai daga kasashen EUHoto: picture alliance/dpa/J. Warnand

Kasashen kungiyar Turai za su kara aza kaimi wajen tisa keyar bakin haure da ke kwarar kasashensu saboda gudun talauci dan mayar da su kasashensu na asali kamar yadda wasu bayanai suka nunar daga kungiyar.

Kasashen na wannan kungiya da ke kallon kwararar baki mafi girma cikin shekaru gwammai na tattaunawa tsawon watanni kan hanyoyi da za su bi wajen ganin an samu raguwar bakin haure da ke shiga kasashen bayan tsallaka tekun bahar Rum daga kasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya da ma yankin Asiya.

A ranar Alhamis ne dai ministoci da ke kula da 'yan gudun hijira daga kasashen na EU za su zauna a kasar Luxembourg dan amincewa da sabbin dabaru da za su bi wajen ganin sun gusar da sha'awar shiga kasashen nasu ta barauniyar hanya.

Ya zuwa yanzu dai a kasashen na Turai kashi 40 cikin dari ne kawai na mutanen da ke zaune a kasarsu ba bisa ka'ida ba aka mai da su gida, da yawa akwai wadanda takardun izinin zamansu a kasashen sun kammala aiki amma suna zaune zaman shahada.