1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta amince da daftarin ficewar Birtaniya

April 29, 2017

Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai sun amince baki daya ba tare da wani jinkiri ba daftarin shawarwarin ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar.

https://p.dw.com/p/2c8Eb
Brüssel EU Gipfel Brexit Verhandlungen
Taron kolin shugabannin kasashen kungiyar EU a BrusselsHoto: Reuters/V. Mayo

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turan Donald Tusk wanda ya sanar da hakan a ranar Asabar din nan a shafinsa na Twitter yace daukacin kasashe 27 na kungiyar ta EU suka amince da jadawalin a taron kolin da suka gudanar a Brussels.

Jami'ai sun ce cikin minti guda shugabannin suka amince da daftarin inda kuma suka kwashe da tafi.

Shi ma shugaban hukumar hadin kan Turai Jean Claude Juncker ya aike da sako ta Twitter yana mai cewa hadin kai ya tabbata.

Ana sa ran mashawarci kan ficewar Birtaniya daga kungiyar ta EU Michel Barnier zai fara tattaunawa kan ficewar bayan zaben majalisun dokokin da Birtaniyar za ta yi a watan Yuni.