1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta bukaci samun kwanciyar hankali a Nepal

April 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2F

Masu fafutukar cigaban dimokraɗiya a Nepal, sun lashi takobin cigaba da zanga zangar adawa ga basaraken ƙasar, sarki Gyanendra, tare da karya shingayen da yan sanda suka gindaya. Wannan sabon ɗauki ba daɗin, ya zo ne bayan ƙaruwar tashe tashen hankula a Katmandu babban birnin ƙasar, a yayin da jamián tsaro suka shiga buɗewa masu zanga zangar wuta da alburusai, inda suka jikata wasu mutane da dama. Tun da farko, gwamnatin ta sanya dokar taƙaita zurga zurgar jamaá domin hana zanga zangar ta nuna adawa da mulkin sarki Gyanendra. A yanzu dai yan adawa da tare da yan tawayen Maoist sun haɗe kai don cigaba da matsin lamba ga sarkin wanda a shekarar da ta gabata ya karbe ragamar mulkin kasar daga hannun yan siyasa. ƙungiyar tarayyar turai ta baiyana takaici da tarzomar dake faruwa inda ta buƙaci sarkin kasar ta Nepal Gyanendra da ya fara tattaunawa da ƙungiyoyin siyasa domin dawo da mulkin dimokraɗiya a ƙasar.