1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kasa cimma matsaya kan 'yan gudun hijira

Gazali Abdou TasawaSeptember 15, 2015

Taron kasashen kungiyar ta EU ya watse baram-baram bayan da wasu kasashen suka ce ba su shirya ba ga karbar adadin 'yan gudun hijirar da shirin ya tanadi tilasta masu dauka.

https://p.dw.com/p/1GWWm
Brüssel - Treffen der EU Innenminister
Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. Wijngaert

Taron kasashen Turai kan batun rarraba 'yan gudun hijira dubu 120 a tsakaninsu da ya wakana a jiya Litanin a birnin Brussels ,ya watse baram-baram ba tare da cimma matsaya guda ba a kan shirin wanda ya tanadi tilasta wa ko wace kasa ta Turai daukar wani kaso na 'yan gudun hijirar.

Ministan harakokin wajen na kasar Luxemburg, Jean Asselborn ya shaida wa manema labarai cewa akasarin kasashen Turan 28 sun amince a bisa manufa su bai wa bakin hauren mafaka a kasashensu ,sai dai sun nunar da cewa a halin yanzu ba su kintsa ba.

Amma dai kasashen Turai sun amince su aiwatar da shirin da suka cimma a cikin watan Yulin da ya gabata da ya tanadi rarraba 'yan gudu hijirar dubu 40 a tsakaninsu. Haka zalika wani ci gaba da aka samu a taron na birnin Brussels shi ne na amincewar da kasashen Italiya da Girka suka yi na bude cibiyoyin gudanar da bincike da kuma rijistan bakin akan iyakokin kasashen nasu.