1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU Aussenminister

Awal, MohammadJuly 22, 2008

Hakan ya zo ne kwana guda bayan cimma yarjejeniyar shiga tattaunawa tsakanin Zanu-PF da MDC.

https://p.dw.com/p/EhZq
Mugabe da Tsvangirai suna musafaha a HarareHoto: AP

A taron su a birnin Brussels a yau Talata ministocin harkokin wajen kasashe 27 na ƙungiyar tarayyar Turai sun faɗaɗa takunkuma akan Zimbabwe inda suka ƙara yawan mutane 37 a jerin jami´an gwamnatin Zimbabwe da aka haramta ba su bisar shiga ƙasashen EU tare da dora hannu kan kadarorinsu.

Tun a farkon wannan wata Birtaniya ta ce zata nemi ƙungiyar tarayyar Turai ta tsaurara takunkumi kan Zimbabwe bayan da buƙatar yin haka ya citura a kwamitin sulhun majalisar ɗinkin duniya, sakamakon kujerar naƙi da ƙasashen Rasha da China suka hau.

Ƙasar Faransa da ke riƙe da shugabancin karɓa karɓa na ƙungiyar tarayyar Turai da kuma wani jami´in ƙungiyar ta EU sun ce an ƙara sunayen ´yan kasuwa 37 da wasu kamfanoni huɗu a Zimbabwe a jerin waɗanda aka hana ba su bisar shiga EU da ɗora hannu kan kadarorinsu. Wannan dai shi ne karon farko da aka ɗauki irin wannan mataki kan ´yan kasuwa da kuma kamfanoni a Zimbabwe.

An dai ba da wannan sanarwa ce a taron ministocin harkokin wajen ƙungiyar ta EU a Brussels duk da sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin shugaba Robert Mugabe da jagoran ´yan adawa Morgan Changirai don share fagen shiga tattaunawa da zumar warwaren rikicin siyasar ƙasar ta Zimbabwe.

A yau ɗin nan ma dai an jiyo shugaba Mugabe yana cewa za su yi aiki tuƙuru musamman kan yiwa kundin tsarin mulkin ƙasar kaskwarima.

Ya ce "A jiya jam´iya Zanu-PF da jam´iyu biyu na MDC sun amince kan yiwa ɓangarori da dama na kundin tsarin mulkinmu canje-canje. Mun kuma amince mu yiwa dokokinmu da dama kwaskwarima."

Majiyoyin jam´iyar Zanu-PF mai jan ragamar mulki da na jam´iyar adawa ta MDC sun yi nuni da cewa a wani lokaci yau Talata sassan biyu za su fara tattaunawa akan shirin raba madafun iko wanda ake fata zai kawo ƙarshen dambaruwar siyasar ƙasar.

Wani jami´in MDC ya ce ra´ayi ya zo ɗaya tsakanin dukkan jam´iyun siyasa da a gaggauta gudanar da wannan taro. A cikin wata sanarwa da ya bayar yau jagoran adawa Morgan Changirai ya bayyana cimma yarjejeniyar da cewa matakin farko ne na wata tafiya da wa´adinta zai dogara kan gaskiya da kuma fatan alheri daga dukkan sassa da abin ya shafa.

Ya ce "wannan ƙoƙari ne da ya shafe mu gaba ɗaya, muna buƙatar juriya don yin sulhu. Dole mu sanya buƙatar Zimbabwe a gaban duk wata tattaunawar da za a yi. A nan kuwa ba zan nuna gajiyawa ba."

Shin ko wannan tattaunawar za ta kai ga kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa. Chris Meroleng manazarci ne kan harkokin siyasar ƙasashen yankin kudancin Afirka ya yi bayani kamar haka.

Ya ce "Idan a ƙarshe aka kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa to haka na zaman wani haɗin kai tsakanin jam´iyun siyasa daban daban a wani yanayi na sulhu da zai kawo canji mai ma´ana da dukkanmu muke fata a Zimbabwe."