1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yaba zaɓen yankin gabacinTimor

April 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuNt

Shugaban ayarin tawagar ƙungiyar gamayyar turai, da su ka sa iddo a zabukan da su ka gudana a yankin gabacinTimor,, Havier Promez Ruiz, ya yaba yadda zaɓen ya wakana ba tare da magudi ba.

A yanzu haka, hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta bada sakamakon kashi 70 bisa 100, na yawan ƙuri´un da aka kaɗa.

Ya zuwa yanzu, yan takara 3 ke sahun gaba, daga jerin yan takara 8, da su ka shiga wannan zaɓe, kuma bisa dukan alamu, sai an kai da zagaye na 2, domin babu wanda zai zarta kashi 50 bisa 100.

A sakamakon ƙuri´un da aka riga a aka ƙirga, a na kunen doki, tsakanin Praminista Jose Ramos Horta, da Fernado de Araujo, inda su ka samu kashi 21, 75 cikin ɗari, sannan Fransisco Guteres na bi masu, da kashi 21, 40 cikin ɗari.