1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yi kira ga Russia da Georgia su yi sulhu

October 2, 2006
https://p.dw.com/p/BuhY

Komishinan harakokin wajen ƙungiyar EU, Havier Solana,yayi kira ga kashen Rasha da Georgia su fahinta juna , bayan rikicin da ya abku a tsakanin su.

Ranar laraba da ta gabata hukumomin Georgia, su ka dakatar da wasu jami´an soja 4, yan ƙasar Rasha, da su ke zargi da leƙen assiri.

Jim kaɗan bayan wannan mataki, Rasha ta maida martani ta hanyar janye jikadan ta, dake Tbilissi, babban birnin Georgia.

Duk da sallamar sojojin da aka yi yau, hukumomin Rasha sun ɗauki saban mataki na katse hulɗoɗin zirga zirga da Geogia.

Shugaban ƙasar Rasha Vladmir Poutine, ya dangata kame sojojin 4, da ta´danci , ya kuma yi alƙawarin shan fansa ta ko wane hali.

Mishel Saakaschwili, shine shugabna yankin yammacin Georgia ya kuma bayyana dalilan gurbacewar danganta tsakanin ƙasar sa, da maƙwabiyar ta, Rasha.

Ƙungiyar gamayya turai, ta bayyana aniyar shiga tsakanin ƙasashen2, don sasanta wannan taƙadama.