1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU tayi Allah wadan amurka,akan wulakanta prisononi a Iraki.

May 14, 2004

Kasashen turai sun fara janyewa daga marawa Amurka baya,a dangane da halin da ake ciki a Iraki.

https://p.dw.com/p/BvjY
Kofar gidan kurkukun Abu Ghraib a kasar Iraki.
Kofar gidan kurkukun Abu Ghraib a kasar Iraki.Hoto: AP

Jamian kasashen turai sun amince dacewa Amurka da Britania sun fice daga jerin kasashe dake fafutukar samar da zaman lafiya a sassa daban daban na duniya,sai dai sun gaza cewa zasu iya tafi da tsarin kasashen Turai din ba tare da tallafin Amurka ba.

Wannan hali da prisononin Irakin suka kasance ciki na wulakanci da tozartawa ya dada kawo shakku cikin raayin turai din,nahiyar da tun a baya ta nuna rashin gamsuwanta da wannan mamaye,A yanzu haka akasarin wadanda suka marawa Amurkan baya a wannan yakin,sun fara ja da baya,a siyasance.

Shugabar jammiyar adawa ta Christian Democrat anan jamus Angela Merkel,wadda ta bada goyon bayanta dari bisa dari wa Amurka a bara dangane da afkawa Iraki da karfin soji,a wannan makon ta bayyana cewa hotunan da aka Bayyanar dangane da halin da Prisononin ke ciki a Iraki,na mai zama babbar Barazana wa Demovcradiyya.A sakamakon goyon bayan da jammiyarta ta bawa Amurka ne ,ya janyo mata kaye a zaben shugaban kasa daya gudana a watan Oktoban shekarata 2002.

Wannan sukan Amurka da shugabar Jammiyar CDU tayi,na mai zama matakin nfarko na janye jammiyar daga wata dangantaka da Amurka.Bugu da kari wasu jamiai na Jammiyar SPD mai mulki da suka marawa Amurkan baya,suma sun fara canja sheka.

Wadannan hotuna da aka yayata ta kafofin yada Labaru ya musguna wa gwamnatin Amurka,wanda kuma kara mata bakin jini ,wadda tuni take ciki,a dangane da manufofin ta na ketare.

Angela tace zai kasance abu mawuyaci Amurka ta maido da martabar datake dashi a idon duniya,kamar yadda ta mayar da kanta yarsandan duniya.wannan dai na mai zama karo na farko da jamian turan suka fito kai tsaye suka soki lamirin na amurka.

A ziyarar daya kai Washinton a wannan makon,ministan harkokin waje na Jamus,Josker Fischer ,yayi kira ga Amurka data mike tsaye wajen dawar da martabarta,da ahalin yanzu ke neman sullubewa,ta hanyar gudanar da cikakken bincike dangane da wulakanta prisononin Iraki da sojojin kasar dana Britania sukayi.

Bugu da Kari Faransa wadda ta kasance cikin jerin kasashe dake adawa da harin na Iraki,ta dada janyewa daga wannan taasa kana abun kunya da sojin Amurka keyi a Iraki.Ministan harkokin wajen Faransa ,yace wadannan hotuna da aka bayyanar ,ya kasance abun takaici da kunya wa Amurka,da kuma yunkuri da akeyi na samarda zaman lafiya a duniya.ya kara dacewa bayan kafa gwamnatin riko a Irakin a karshen watan gobe,a bawa gwamnatin daman gudanar da zabe da kanta cikin adalci a watan Janairun shekarata 2005,ga mai rai.To sai dai ministan harkokin wajen na Amurka ya dada jaddada cewa ,kasarsa bazata tura dakarunta zuwa iraki ba,koda MDD ta maye gurbin Amurka da kawayen ta a Iraki. Yace ,abunda Faransa zata iyayi shine horar da yansandan Irakin,tattauna batun bashi da ake bin kasar a ketare ,tare da taimakawa sabuwar gwamnatin kasar,kafa dangantaka mai nagarta da Turai.

Bugu da kari sabon prime ministan Poland,Marek Belka na cigaba da fuskantar matsin lamba na yanke waadin cigaba da kasancewar dakarun kasar a kasar ta Iraki,daga Alummar kasarsa.Daman dai sabon Prime ministan Spain Jose Zapatero ya janye sojojinsa daga wannan kasa,Abunda ke dada tabbatar da yadda kasashen turai ke janyewa daga Amurkan.

Zainab AM Abubakar.