1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta horas da sojojin Afirka ta Tsakiya

Gazali Abdou TasawaApril 19, 2016

Kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar a wannan Talata da wani shiri na horas da sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya 200 wadanda za su maye gurbin sojojin Faransa na rundunar Sangaris a Afirka ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/1IYVM
Zentralafrikanische Republik UN Soldaten
Hoto: picture-alliance/AA/H. Serifio

Kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar a wannan Talata da wani shiri na horas da sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wadanda za su maye gurbin takwarorinsu na kasar Faransa mambobin rundunar zaman lafiya ta Sangaris da ma sauran sojojin Majalisar Dinkin Duniya masu aikin maido da zaman lafiya a wannan kasa wacce ta share shekaru uku tana fama da yakin basasa.

Sabuwar rundunar tsaron ta sojojin jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar mai kunshe da mambobi 200 za ta maye gurbin rundunar sojin kasa da kasa wacce wa'adin aikinta ke kawo karshe a karshen watan Yuli mai zuwa.

Rundunar za ta gudanar da aikinta ne a birnin Bangui a tsawon wa'adin shekaru biyu inda za ta mayar da hankali ga horas da sojojin kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kan sanin makamar aikin soja a karkashin tafarki na demokradiyya.