EU za ta kai Faransa kotu
September 29, 2010Talla
Hukumar Tarayyar Turai ta ɗauki matakan gabatar da ƙasar Faransa a gaban kotu, sakamakon saɓa dokar 'yancin walwala ta Tarayyar Turai, inda Faransa ta kori 'yan ƙabilar Roma dake ƙasar ta. Kwamishiniyar shari'a ta ƙungiyar Tarayyar turai wato EU, Viviane Reding ta ce Faransa ta karya doka, bayan tilastawa 'yan ƙabilar Roma kimanin dubu takwas (8000) da su fice daga ƙasarta, kana ta tasa ƙiyarsu izuwa ƙasashensu na asali wato Romaniya da Bulgariya. Wannan matakin gabatar da Faransa gaban kotu zai shafi dangantakar Faransa da EU sosai, kasancewa shugaba ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya ƙeƙesa ƙasa, ya kare korar baƙin.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi