1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU zata tallafa wa Afirka a fannin tsaro

Salissou Boukari/ MABJuly 6, 2016

Kungiya Tarayyar Turai na kokarin kaddamar da wani tsari na bayar da horo ga sojoji a kasashen Afirka da ke fuskantar kalubalen tsaro da na kwararar 'yan gudun hijira

https://p.dw.com/p/1JKJ4
Zentralafrikanische Republik Sangaris-Soldaten Polizist 09.02.2014
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Wannan tsari da a halin yanzu yake a matsayin tantancewa a cikin Kungiyar ta Tarayyar Turai, na nufin samar da isassun makammai da kudadensu ya kai miliyan dubu biyu da miliyan 300 na Euro ga kasashen na Afirka. Kuma burin da aka sama a gaba shi ne na samar da kwanciyar hankali a cikin kasashen da ke mu'amala da Tarayyar Turai har ya zuwa shekara ta 2020.

Sai dai a cewar Evariste Ngarlem Tolde Malami a Jami'ar birnin Ndjamena na kasar Chadi kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, wannan ba wata mafita ba ce mai inganci kasashen na Turai suke shirin dauka.

" Abin da ke kawo zaman lafiya, shi ne tafiyar da kyaukyawan mulki, tafiyar da kyaukyawan tsarin albarkatun kasa, da kiyaye 'yancin dan Adam. Hakan kuma kan iya kaiwa kasa ta samu ci gaban da ake bukata."

Sai dai kuma hakan ya sha bamban da tunanin wasu membobin kwamitin na Tarayyar Turai, inda suke ganin hakan ya fice tunani, a ce za a bunkasa kasar da ke fama da tashe-tashen hankulla. Wannan tunanin ya zo daidai da na Docta Boubakar Hassane Masanin harkokin shari'a kuma malami a Jami'ar Abdoulmoumouni ta Birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.

AMISOM - Soldaten in Somalia
Sojin Afirka za su samu horo daga EUHoto: picture alliance/AP Photo/Jones

" Barazanar da ake fuskanta a fannin tsaro batu ne wanda yake na hakika. Shugabannin kasashen Yamma babu wani tsari mai inganci da suke yi na ganin an kawo karshen kungiyar Boko Haram, domin idan aka kwatanta yankunan da ake fuskantar tashe-tashen hankula, kasashen Yamma sun fi bada karfi kan abin da ke gudana a kasashen Siriya da Iraki."

Kasashen da ke da hulda da Tarayyar Turai kamar su Mali, Somaliya, sun samu taimako da ya basu damar samar wa sojojinsu kayan aiki a shekara ta 2015 ba. Sai dai manazarta na ganin cewa wannan mataki ba zai bada damar kaiwa ga burin da ake son cimma ba, ganin yadda kalubalen yake da tarin yawa musamman ma a fannin tsaro wanda kuma ya wajaba ga dukannin bangarorin biyu.